Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taliban Ta Musanta Cewa Tana Da Hannu A Harin Kabul


Tashar talabijin din ta ci gabata da gabatar da shirye shiryenta bayan wani tsaiko, tare da cewa harin da aka kawowa Shamshad TV ya zo karshe

Wani harin bomb da kuma bindigogi da aka kai hedkwatar wata tashar talabijin mai zaman kanta dake birnin Kabul a Afghanistan yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyu da raunana mutane fiye da ashirin.

Kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai hari kan tashar da ake kira Shamshad TV dake birnin.

Shaidu sun baayyana cewa harin da aka kai da safiyar yau talata ya fara ne da abunda ake zaton kunan bakin wake ne , wanda ya baiwa wadansu maharani damar kutsawa cikin tashar.

An ji Karar wasu fashe-fashe har sau uku lokacin kawanyar data dauki sa’o’I kafin daga bisani jami’an tsaron Afghanistan suka samu nasarar harbe maharan.

Tashar talabijin din ta ci gabata da gabatar da shirye shiryenta bayan wani tsaiko, tare da cewa harin da aka kawowa Shamshad TV ya zo karshe.

Taliban ta musanta cewa tana da hanu a kai wannan hari.

A halin da ake ciki kuma babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, yace sansanonin Taliban da suke Pakistan “babban kalubale ne” ga kokarin da ake yi na kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afghanistan

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG