Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tantama Akan Zaben Pakistan


Ana ci gaba da tantama akan sahihancin zaben kasar Pakistan mako guda bayan zaben da aka gudanar a kasar, inda fitaccen dan wasan cricket da ya shiga siyasa Imran Khan ya yi ikirarin nasara.

Wasu daga cikin shuwagabanin manya manyan jam’iyyun siyasan sun hadu tare da wasu jami’iyyun a babban birnin na Islamabad don nuna rashin amincewarsu da zaben da suka ce an tafka magudi. Duk da haka sun ce zasu yi aiki a majalisar su kuma fiddo nasu dan takarar don yayi takara da Khan a matsayin firam minista.
Ba zamu amince da sakamakon wannan zaben ba da kuma hukumar zaben a cewar Sherry Rehma, wata shugabar jami’iyyar Pakistan people party, jami’iyyar firam ministan da aka kashe Benazir Bhutto. Zamu ci gaba da zanga zanga akan wannan sakamakon zaben a ciki da wajen majalisa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG