Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taraba: An Nada Sabon Kpanti Zing


Nadin Sauratar tsohon Ministan tsaron Najeriya, Theophilus Danjuma in Zaria, Kaduna State.
Nadin Sauratar tsohon Ministan tsaron Najeriya, Theophilus Danjuma in Zaria, Kaduna State.

Gwamnatin jihar Taraba ta baiwa  sabon sarkin  al’uman Mumuye da ke jihar Taraba   Kpanti Zing Alh. Suleiman Ibrahim sanda mai daraja ta daya a matsayin Kpanti na bakwai.

An yi bukuwan nadin sarautar ne a yau Asabar a birnin Jalingo wanda hakan ke nufin sabon sarkin ya maye gurbin wanda ya rasu a shekarar da ta gabata.

Da yake jawabin rantsar da sabon Kpanti Zing a dakin majalisar zartaswa, Gwamnan jihar Taraba Arch, Darius Dickson Ishaku ya ce gwamnati ba za ta lamunci masu neman wargaza kokarin gina kasa da ta ke yi, ta hanyar ruruta kiyayya da kyama sakanin al’uma ba.

Sabon Kpantin ya fada a hirar da wakilinmu ya yi da shi cewa yana fatan amfani da karbuwar da ya samu wajen masu nadin sabon sarki.

Alhaji Ibrahim ya yi takarar ce da mutane da dama bayan rarrabuwar kawuna da ya kunno kai lokacin gwagwarmayar neman kujerar.

Saurari wannan rahoto na wakilin Muryar Amurka Sanusi Adamu domin jin yadda nadin sarautar ya kankama:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG