Accessibility links

Taraba: An Zargi Gwamnan da Yin Anfani da Takardun Bogi


Senator A'ishah Jummai Alhassan, 'yar takarar kujerar gwamnan Taraba a karkashin jam'iyyar APC

Yayinda kotun sauraran karakin zabe ke sauraran karar da aka shigar na kalubalantar zaben gwamnan jihar Taraba , wata sabu kuma ta kunno kai.

Wasu 'yan takaran gwamna su biyu sun garzaya babban kotun tarayya suna kalubalantar gwamnan jihar Architect Darius Isyaku bisa zargin cewa ya mika takardun bogi yayinda ya tsaya takara.

Wadanda suka garzaya kotun sun hada da dan takarar jam'iyyar Action Alliance, ko AA, Mr.Pari Charles Buki da takwaransa na jam'iyyar United Democratic Party ko UDP, Onarebul Gambo Usman.

Mr Pari Charles Buki yace sun garzaya kotun ne saboda akwai wasu abubuwa da suka gano daga takardar da gwamnan ya cika yayinda ya mika takardar tsayawa takara. Yayi karyar kan inda aka haifeshi. Yayi karya kuma dangane makarantar sakandare da ya je.

Shi ma Onarebul Gambo Usman yace suna nan daram sai sun ga abun da ya tubewa buzu nadi. Yace sun gano karerayi da yawa a cikin takardun da ya cika domin tsayawa zabe. Yace mafi yawan takardun da gwamnan ya cika na bogi ne. Ya nemi a saukar da gwamnan kana a sake gudanar da wani zaben.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kotun dake sauraran karar da 'yar takarar gwamna a karkashin APC Sanata Aisha Alhasan ta shigar ke zamanta a Abuja. To saidai gwamnan jihar ta bakin kakakinsa Alhaji Hassan Mijinyawa yace shi bai razana da kararrakin da aka shigar gaban kotuna ba.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

XS
SM
MD
LG