Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarayyar Turai Ba Zata Kakabawa Rasha Takunkumi Ba Akan Siriya-Mogherini


Federica Mogherini sakatariyar harkokin wajen Kungiyar Tarayyar Turai

Babbar jami'ar hulda da kasashen waje ta tarayyar turai, Federica Mogherini, tace kungiyar bata tunanen saka wa Rasha takunkumi sakamakon shigshigin da ta keyi a Syria.

A yau Litinin ta bayyanawa manema labarai a Luxembourg cewa babu wata memba da ta nuna bukatar yin hakan.

Mogherini tace an tattauna akan saka takunkumi akan wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin Shugaban kasar Syria Bashar Al-Asad, sannan sun jaddada bukatar wadanda suke da hannu a al’amuran dake faruwa a Syria da su samar da hanyar da za’a tattuna domin warware matsalar.

Bayanin nata yazo ne kwana guda a bayan da Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yayi gargadi akan yiyuwar saka tankunkumi akan abubuwan da suka shafi Syri, sannan ya fito da kakkausar harshe yana sukar lamirin irin matakan sojan da Rasha take dauka a Syria.

Wannan batu na Syria shine ya kanainaye tattaunawar da shi Kerry yayi jiya lahadi da ministan Harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson da Mnistan Harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da wasu jami'an diflomasiyyar.

A ranar Lahadi Kerry ya bayyana cewa jami’ai sun damu matuka da tashin hankalin da ya sami Arewacin Birnin Aleppo.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG