Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Musunta Zargin Cewa Tana Kaiwa Amurka Hari Ta Duniyar Gizo


Shugaban Rasha Vladmir Putin ya musunta sabon zargi Amurka na cewa ita Rasha din tana kaiwa Amurkan hari a yanar gizo, kuma tana ba’a a kan barazanan daukar fansa da Amurka take yi idan Rasha tayi mata shisshigi a harkokin zaben Amurka dake tafe.

A wani jawabin telbijin da Putin yayi a wani taron manema labarai a jiya Lahadi a India, yace zancen tuhumar kutsen sakonnin email, wani kokari ne da hukumomin na Amurka ke yi don janye hankalin Amurkawa daga abinda ya kira “tarin matsalolin” da Amurka ke fama dasu.

Kalaman na Putin sun zo ne kasa da kwanaki biyu da mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ya aike da sakon kashedi ga Shugaba Putin.

Mr. Biden ya shaidawa tashar telebijin ta NBC a ranar Juma’a cewa, ramuwar gayya da Amurka zata yi a kan harin yanar gizo da da Rasha ke yiwa Amurka, zai zo a lokaci na zabin ransu kuma daidan lokaci da zai yi babban tasiri.

XS
SM
MD
LG