Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarihin Rantsar da Shugabannin Amurka


Wasu tsoffin shugabannin Amurka. Daga hagu Reagan da Bush uba da Bush da

An da de ana rantsar da shugabannin Amurka amma a shekarar 1961 lokacin da aka rantsar da Shugaba John F. Kennedy ne aka soma salon da har yanzu ake anfani dashi kuma ko yau ma salon za'a bi wurin rantsar da Donald Trump da zai zama shugaba na 45

A jawabinsa shugaba John Kennedy yace abun da yayi imani dashi zai iya tsorata mutum shi ne tsoro.

John Kennedy shi ne shugaban Amurka na 35 kuma a lokacin ya kara karfafawa matasa gwuiwa akan kishin kasa. Yace 'yanuwana Amurkawa kada ku dinga tunanin abun da gwamnati zata yi maku amma ku yi tunanen abun da zaku yiwa kasarku.

Shekaru ishirin bayan an rantsar da John Kennedy shugaban Amurka na 40 Ronald Reagan ya dare kan karagar mulkin kasar da shan alwashin rage girman gwamnati ko yadda ake gudanar da harkokin gwamnatin Amurka.

Reagan yace a wannan lokaci da kasa take fama da matsaloli ko kuma rikici gwamnati ba zata iya magance matsalarta ba, a zahiri ma gwamnatin ita ce matsalar.

Shi ma Donald Trump bayan da ya lashe zabe a watan Nuwamban bara na bazata yace wannan lokacin doki ne ko murnar cewa yana da rai. Yace kaddara ta riga ta faru amma shinan gaibu kuma sai Allah. Yace amma a karon farko cikin lokaci mai tsawo ba'a san hakan zata faru ba.

Bisa tarihi a nan Amurka lokacin rantsar da sabon shugaba lokaci ne da ake mantawa da banbancin siyasa domin dorewar mulkin dimokradiya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:08 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG