Accessibility links

Taro Kan Cutar Polio A Arewa Maso Gabashin Nijeriya

  • Ibrahim Garba

Wasu yara a wani gangamin yaki da cutar polio a arewacin Nijeriya

Mata da wasu da abin ya shafa masu yawa ne dai su ka halarci taron yaki da cutar polio da Muryar Amurka ta shirya a birnin Maiduguri.

Mata da maza da wasu kwararru da dama ne dai su ka yi ta bayyana ra'ayoyinsu a wani taron musayar ra'ayi game da ingantattun hanyoyin yaki da cutar shan inna ko polio da Muryar Amurka ta shirya a birnin Maiduguri.
Taron, wanda aka shirya don arewa maso gabashin Nijeriya ya ga dinbin jama'a, wadanda su ka yi ta bayanai game da cutar da kuma hanyoyi daban daban na yakarta.
Jagoran wakilanmu na harkokin lafiya Nasiru Yakubu Birnin Yero, ya ruwaito wata uwa mai suna Malama Zulai Abdullahi Gaya na bayya na yadda ta yi ta fama da jinyar diyarta mai suna Adama sanadiyyar wannan cuta ta polio. Malama Zulai ta bayyana yadda rashin allurar rigakafi ya sa ta yi ta zuwa wurare daban daban neman magani. Ta ce har kasar Turai ta je amma a banza. Ta na mai kiran da a rinka amsar rigakafin a lokacin da ya dace kuma bisa ka'ida. Haka zalika, wata shugabar kungiyar mata Musulmi ta FOMWAN mai suna Malama Asabe Ali ta ce kungiyarsu ta himmantu ga yaki da wannan cutar duk ko da rashin fahimtar da wasu mutane ke fama da shi game da cutar. Ita ma wata shugabar kungiyar mata 'yan jarida (NOWAJ) mai suna Maimuna Garba ta ce za su cigaba da fadakar da jama'a.
XS
SM
MD
LG