Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taro kan Rikicin Fulani da Tibabe


Fulani makiyaya
Fulani makiyaya
Sanadiyar rikicin Fulani makiyaya da manoma a jihohin Benue da Nasarawa da Taraba da wasu wuraren gwamnonin dake makwaftaka da juna sun yi taron fahimtar juna kamar yadda mukaddashin gwamnan jihar Taraba ya tabbatar.

Yace sun zauna da gwamnonin kuma ta gefensu suna kokari su ga an kawo karshen tashin tashinar. Yace ana zagayawa ana gayawa mutane su zauna lafiya da junansu yace su ma a Taraba suna nan suna kokari. Yace duk su gwamnonin sun fahimci juna domin dama an basu hakin mutanen kuma yakamata su rikesu a matsayin amana su kuma tabbatar sun zauna lafiya.

To saida kawo lokacin da gwamnonin suka yi taronsu ana samun harin sari ka noke a wasu yankunan jihar Taraba inda wasu ke ketarowa daga jihohin dake makwaftaka da ita su kai hari cikin kauyuka musamman a yankin Ibi. Isiyaka Adamu shugaban karamar hukumar Ibi ya bayyana matakan da suke dauka domin harin sari ka noke da ake kaiwa kan kauyukansu. Yace sun sanarda gwamnatin jiha kuma an kara masu jami'an tsaro dake yin sintiri yanzu. Sai dai yace akwai dazuzuka munana da jami'an tsaro basa iya shiga. Cikinsu ne wasu kauyuka suke da ake kaima hari.

Masarautar Donga dake kudancin jihar ta shirya taron sulhu tsakanin Fulani da Tibabe domin samun zaman lafiya. Sarkin Donga ya kirawo shugabannin Fulani da na Tibabe da jami'an tsaro inda ya nemi su zauna lafiya a masarautarsa.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG