Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Agaji ta Mata a Kano ta Tara Kayan Agaji Zuwa Borno da Yobe


Mata dake neman taimako
Mata dake neman taimako

Biyo bayan munanan hare hare da aka kai wasuwurare da dama a jihohin Borno da Yobe lamarin da ya saka dubun dubatan mutane cikin wahala wata kungiyar agaji tana tara kayan da zata kaimasu.

Abokiyar aiki Hajiya Halima Djimrao ta samu ta zanta da Hajiya Asmau Yahaya wata shugabar kungiyar agaji a Kano bisa ga kokarin da suke yi domin su taimakawa wadanda rikici ya rutsa dasu a jihohin Borno da Yobe.

Hajiya Asmau Yahaya tace sun fara tara kaya kama daga tufafi zuwa kayan abinci da na gyaran muhalli su samu su aika Damaturu a jihar Yobe da kuma Maiduguri a jihar Borno. Tace da sun tara zasu fara aika da motoci da kayan da suka tara.

Suna karban kaya iri-iri wadanda ba zasu rube ba kafin a raba su. Suna da wuraren da suke tara kayan a birnin Kano. Idan kuma kudi mutane zasu bayar akwai yadda zasu aika da kudin. Akwai hanyoyin bada sako ko ta waya ko ta yanar gizo ko kuma ta aikawa kai tsaye a wuraren da aka kebe.

Hajiya Asmau Yahaya ta kira jama'a su yiwa Allah da Annabinsa su taimaki wadanda wannan bala'in ya farmasu da fatan Allah zai dauke wa kasar bala'in nan ba da dadewa ba.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:37 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG