Accessibility links

Taron Addu'ar Zaman Lafiya

  • Ibrahim Garba

Wasu 'yan gudun hijirar tashin hankalin arewa maso gabashin Nijeriya.

Wata Kungiya mai goyon bayan Shugaban Nijeriya ta shirya abin da ta kira addu'ar neman Allah ya kawo zaman lafiya a arewa maso gabashin Nijeriya.

Wata kungiyar goyon bayan Shugaba Goodluck Jonathan na Nijeriya mai Suna “Transformation Ambassadors of Nigeria (TAN) a Turance, ta shirya wani taron addu’ar Allah ya kawo zaman lafiya a arewa maso gabashin Nigeria a garin Gombe.

Shugabannin addinai da na al’umma sun yi ta addu’o’in da bayyana fatan Allah ya maido da zaman lafiya a arewa maso gabashin Nijeria. A jawabinsa, Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Dankwambo ya bayyana taron da cewa ba gwamnati ce ta shirya ba, wata kungiya ce mai zaman kanta, wadda ta kunshi mutane daga jam’iyyu daban daban, ta shirya taron don addu’ar Allah ya kawo zaman lafiya a arewa maso gabashin Nijeriya.

Saidai kuma wani mai suna Alhaji Garba Tela y ace taro ne na siyasa, inda mutane daga jihohi shida su ka taru suna ta tallata sunan Shugaba Jonathan.

Ita kuma Kwamishiniyar mata Hajiya Saadatu Mustapha ta ce kowa na da damar bayyana ra’ayinsa a tsarin dimokaradiyya.

XS
SM
MD
LG