Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Dakarun Amurka Da Takwarorinsu Na Yankin Tafkin Chadi a Yamai


Sojojin Tafkin Chadi Da Takwarorinsu

A Jamhuriyar Nijar yau wasu hafsoshin sojan kasashen yankin Tafkin Chadi da Jamhuriyar Benin tare da adin gwiwa da kwamandojin cibiyar tsaro ta AFRICOM, da na Faransa da Ingila na gudanar da taron kwanaki biyu.

Ana gudanar da taron kwana biyu ne, da nufin karawa juna sani akan dubarun harhada bayanan sirri, a ci gaba da neman hanyoyin murkushe ayyukan kungiyar Boko Haram da ISIS a yankin Tafkin Chadi.

Lura da mahimmancin bayanan sirri a yaki makamancin wanda kasashen na Tafkin Chadi ke kwabzawa, da kungiyoyin ta’addanci shekara da shekaru, ya sa cibiyar tsaro ta kasar Amurka a nafiyar Afirka, wato Africom shirya wannan taro.

Manufar taron ita ce a karawa juna sani akan dubarun samar da bayanan sirri a wannan lokaci da bayanai ke fayyace babbar alakar da ke tsakanin Boko Haram da kungiyar ISIS.

Mataimakin darekatan ofishin kula da horo a ma’aikatar tsaron Najeriya, Major Janar C.A Abraham, na daga cikin masu halartar wannan taro.

Ya kuma bayyana matsayin kara karfafa hadin kan da ke tsakanin kasashen Tafkin Chadi da Jamhuriyar Benin da kasashe aminai masu yaki da ta’addanci.

Taron wanda za a shafe kwanaki biyu ana gudanarwa, a wani bangare zai kasance wata damar kara lakantar dubarun amfani da jiragen saman da kasar Amurka ta bai wa wadanan kasashe, a matsayin wata ingantattar hanyar hango abokan gaba in ji Janaral N’Gare Adoum shugaban ma’aikatar samar da bayanan sirrin sojan kasar Chadi.

Domin jin cikakken bayani, saurari rahoton da wakilinmu Souley Moumouni Barma ya aiko mana da Yamai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Facebook Forum

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Aminu Saira

Aminu Saira
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Karin bayani akan Nishadi
XS
SM
MD
LG