Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Fahimtar Juna Tsakanin Sojojin Najeriya Da ‘Yan Jarida


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Rundunar tsaron Najeriya ta sha alwashin gamawa da burbushin yan Boko Haram nan ba da jimawa ba.

Ya yin taron bita na kwana ‘daya da aka gudanar ga ‘yan jaridun da ke ‘dauko labaran tsaro, babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya, Janar Abayomi Olonisakin, yace dakarun kasar zasu yi duk wani abu mai yiwuwa don tabbatar da sun gama da ‘dan abin da ya rage na burbushin mayakan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Janar Olonisakin, wanda Rear Admiral Jonathan Ango ya wakilce shi a wajen taron, ya yaba da rawar da ‘yan jaridu ke takawa a wajen kokarin cin lagon ‘yan ta’adda a kasar. Amma duk da haka ya nemi ‘yan jarida da a koda yaushe su rika tantance gaskiyar lamari daga hedikwatar tsaron kasar.

Yin aiki tare tsakanin sojoji da ‘yan jaridu kusan shine batun da yafi mamaye taron. Babban bako mai jawabi a wajen taron shine kwararre kan sha’anin tsaro Dakta Egan Onoja, wanda yace akwai bukatar hadin kai tsakanin sojoji da ‘yan jaridu wanda hakan zai taimaka sosai.

A baya dai sojoji na zargin ‘yan jaridu da ‘karin gishiri wajen bayar da rahotannin tsaro, yayin da ‘yan jaridun ke cewa sojojin na jan ‘kafa wajen ba da bayanai, amma yanzu an fara ganin bangarorin biyu suna ‘dasawa suna aiki tare.

Shugaban kungiyar ‘yan jaridun Najeriya Paul Ela, yace yanzu sun fahimci yadda sojoji ke aiki, haka kuma yayi kira da a ci gaba da hada kai tsakanin ‘yan jaridu da sojoji.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG