Jagorar bangarori da kuma jami'an diflomasiyya daka kasashe sama da 20 da su ka yi taro jiya Talata a Birnin Paris sun cimma amincewa bisa manufa cewa kasar Libiya ta arewacin Afirka ta gudanar da zabe a karshen wannan shekarar.
Wannan taron shi ne karo na biyu da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi yinkurin kawo zaman lafiya a Libiya.
Macrone ya yaba da matsayar da aka cimma, ya na mai cewa wani gagarumin cigaba ne a yinkurin da ake yi na samar da zaman lafiya a Libiya. "Yanzu dai ta bayyana cewa mun dukufa wajen taimakomn wannan kasar, da kuma jadawalin gudanar da zabukan majalisar dokoki da kuma na shugaban kasa" a cewarsa.
Shugaban gwamnatin "hadin kai" wadda kasashen duniya ke goyon baya mai mazauni a birnin Tripoli, Fayez al-Sarraj, dan shekaru 75 da haihuwa da Khalifa Haftar, wanda dakarunsa su ke da karfi a gabashin kasar, da kuma Kakakin Majalisar dokokin kasar da ke garin Tobruk na gabashin kasar sun cimma amincewa cewa Libiya ta gudanar da zabe ranar 10 ga watan Disamba, a cewar jami'an kasar Faransa.
Facebook Forum