Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Ta Gargadi Amurka Kada Ta Kara Takunkumai A Kan Iran


Macron da Trump
Macron da Trump

Ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian ya fada a yau Laraba cewa idan Amurka ta kuskura ta dorawa Iran wani sabon takunkumi, zai kara jefa gabas ta tsakiya cikin rikici.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya yi barazana farkon wannan mako cewa, za a dorawa Iran mummunar takunkumin kudi da ba a taba ganin irinsa ba, idan bata sake halayenta ba, inda ya lissafo jerin bukatu 12 a kan sabuwar yarjejeniyar nukiliya.

Le Drian ya fadawa wani gidan rediyon kasar ta France Inter cewa, dora sabbin takunkumai ba zai karfafa tattaunawa ba, sai dai ma zai taimakawa ra'ayin rikau na Iran, yayin da kuma zai raunana shugaba Hassan Rouhani.

Yace wannan matsaya da Amurka ta dauka nada hadarin gaske ga yankin.

Bugu da kari a kan shirin nukiliyar Iran da ayyukanta a yankin, Pompeo ya lashi takobin maido da Amurkawa da aka yi garkuwa dasu a Iran.

Facebook Forum

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG