Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Kokarin Hakan Man Fetur a Jihohin Arewa Goma Sha Uku


Gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu
Gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu

Tun da jimawa ake harsashen akwai man fetur kwance a kasa a wasu jihohin arewa to sai dai gwamnatin tarayya ce kadai take da ikon yin wani abu a kai.

Wakilan gwamnoni goma sha uku dake arewacin Najeriya sun gudanar da wani taro a Minna babban birnin jihar Neja da nufin kara kaimi a kan shirin samarda man fetur a yankin arewa.

Mahalarta taron dukansu kwamishanonin ma'aikatun ma'adanan kasa ne a jihohin goma sha uku. Sun ce bincike ya nuna cewa jihohinsu nada man fetur. Alhaji Dahiru Maishanu kwamishanan ma'adanai na jihar Sokoto ya ce makasudin taron shi ne jihohin da aka samu alamu akwai danyan man fetur su hada kai bisaga umurnin gwamnoninsu su ga yadda zasu bada shawara dangane da ayyukan da ya kamata su yi. Ya ce duk abubuwan da suka shirya zasu kaiwa gwamnoninsu kana su ma su kaiwa gwamnatin tarayya domin a ga yadda za'a yi a soma hako man domin uunfanin Najeriya gaba daya.

Kamar jihar Neja bincike ya nuna cewa a yankin Bida an gano mai wanda kashi talatin fetur ne kana kashi saba'in iskar gas ce. Kwamishanan ma'adanai na jihar Alhaji Abubakar Jibril shi ya bayyana hakan. Ya ce inda suka tsaya gwamnatin tarayya ita ce zata cigaba. Idan kuma gwamnatin ta ce bata da kudin yin aikin tana iya bari su nemi masu tsaka jari su cigaba da aikin.

Mr Abubok Agwam kwamishanan ma'adanai na jihar Filato ya bayyana dalilin da ya sa ana samun jinkiri wurin soma hakar man tun da a tabbatar akwai shi a arewa. Ya ce akwai damuwa da yawa a Najeriya. Kowace gwamnati akwai abun da ta fi ba mahimmanci da take son ta yi. Ya ce to amma kan mage ya waye idanunsu sun budu domin jihohin kudu sun fara yiwa arewa hannunka mai sanda cewa watarana zasu hana arewa man fetur. Ya ce wajibi ne yanzu arewa ta tashi ta nemi nata. Ya ce dalili ke nan duk jihohin arewa suka hada kai kan wannan lamarin, wato a tafi tare domin a rayu tare.

Masani kan harkar man fetur wanda ya shugabanci kwamitin bincike da gwamnatin jihar Neja ta kafa Injiniya Yusuf Yabaji Sani ya yi karin haske a kan adadin man.Ya ce idan gaskiya za'a bi man dake jiha daya kawai ya isa Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG