Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Gargadin ‘Yan Najeriya akan Magungunan Jima’i


Mutane na amfani da dakan maza na zamani a Najeriya ba tare da sharrudan likitoci ba.
Mutane na amfani da dakan maza na zamani a Najeriya ba tare da sharrudan likitoci ba.

Hukumar kula da magunguna da abinci ta Najeriya, wato NAFDAC ta koka akan yadda ‘yan Najeriya ke yawan amfani da magungunan jima’i na turawa.

Dr. Mohammed Ladan wanda yake yawan tattaunawa da Sashen Hausa yayi karin haske akan illar wadannan magunguna.

Dr. Ladan yace “Illar maganinnan, kasan akwai wasu mutane masu ciwon zuciya, ko masu ciwon hawan jini, akwai wasu irin magunguna da suke sha, to idan aka hada wadannan magungunnan da shi wannan dakan maza da mutane ke sha, yakan saka zuciyar mutum ta samu illa. Kuma akwai wasu idan basu yi sa’a, sai su shafi idanunsu. To duk wadannan idan suka hadu taru, akwai illa sosai”.

“Magungunan, abunda suke shine bude hanyar jinni. Wani lokacin sai ya bude hanyar jinin yayi yawa, yadda ba’a iya rike shi. Idan abun ya samu, babu yadda za’ayi a gyara abun”, in ji Dr. Ladan.

Dr. Ladan ya bada shawara. “Abunda zan cewa mutane shine, kafin ka soma amfani da maganin, ka je kayi magana da likitanka, ya duba ya tabbatar baka da wani larura kuma, musamman yawancin mu kasan muna da irin ciwon zuciya, da ciwon hawan jini, bamu san muna da su ba”.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:54 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG