Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Koli Akan Malaria Ya Bukaci A Kara Kaimi Wajen Yakinta


Bill Gates daga hagu yana tattaunawa da Yarima Andrew da Charles a wurin taron koli akan Malaria da aka yi a London, Afirilu 18, 2018.
Bill Gates daga hagu yana tattaunawa da Yarima Andrew da Charles a wurin taron koli akan Malaria da aka yi a London, Afirilu 18, 2018.

A taron kolin da aka yi akan Malaria hamshakin attajirin da ya taimaka da makudan kudi wajen yaki da cutar ya ce idan ba'a tashi tsaye ba an hada karfi da karfe wajen yakar cuta zata dawo ta dinga kashe mata masu juna biyu da yara a nahiyar Afirka ta dalilin haka ya sake jaddada bada wasu makudan kudi

Bayan an shafe shekaru 16 da aka samu raguwar maleria ainun, cutar ta sake kunno kai a duniya kuma masana sun yi kashedi cewa, sai an kara kaimi wurin daukar matakan dakile cutar, in ba haka ba nasarorin da aka samu a baya zasu je a banza. Wakilin Muryar Amurka Henry Ridgwell ne ya aiko da wannan rahoto daga taron koli a birnin London inda aka yi kira ga wakilai dake halartan taron su karfafa bada tallafi ga shirye shiryen yaki da malaria a duniya.


A shekara ta 2016 al’amari ya canja. An bada rahoton cewa sama da mutane miliyon 216 suka kamu da zazzabin cizon sauro a kasashe casa’in, an samu karin mutane miliyon biyar a kan shekara ta 2015.


Hamshakin attajirin nan Bill Gates,wanda ya taimaka ainun wajen yaki da zazzabin cizon sauro ya fadawa mahalartar taron kolin cewa idan bamu kirkiro da sababbin hanyoyi ko dabaru ba, zamu samu koma baya. Idan bamu ci gaba da kara kaimi kamar yanda muke yi a yau ba, malaria zata dawo kuma ta kashe kananan yara sama da miliyon guda a shekara, saboda magungunan cutar da maganin sauro basu iya kashe sauron da kuma kwayar cutar ba.

An kiyasta cewa, maleria tana yiwa tattalin arzikin Afrika illar dala biliyon 12 a duk shekara kuma tana lakume kashi 40 na kasafin kudin harkokin kiwon lafiyar kowace kasa a nahiyar. Kananan yara da mata masu juna biyu ne cutar tafi addaba ko kuma ta fi yiwa illa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG