Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Kolin Da Shugabannin Amurka Da Koriya ta Arewa Ke Shirin Yi Yana Tanga-tanga


Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jon Un
Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jon Un

Yayinda ake ci gaba da taron kolin shugabannin Amurka da Koriya ta Arewa da aka shirya yi waan gobe, Shugaban Amurka bashi da tabbas taron zai wakana kodayake sakataren harkokin wajensa Mike Pompeo ya fishi karfin gwuiwar cewa taron zai yiwu

Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce a makon gobe idan Allah ya kaimu za'a sani ko zai gana da takwaran aikin sa na kasar Korea ta Arewa Kim Jon Un a ranar sha biyu ga watan Yuni a kasar Singapore ko kuma a'a.

Tunda farko shugaba Trump ya fada cewa idan ba'a cimma daidatuwa na yin taron kolin a ranar sha biyu ga watan Yuni ba, to za'a yi a wata ranar da bai bayana ba

Itama Korea ta Arewa ta nuna alamar cewa zata janye daga halartar taron kolin a saboda bukatun Amurka akan shirin nukiliyar kasar.

Jiya Laraba sakataren harkokin wajen Amurka ya fadawa kwamitin harkokin kasashen waje na Majalisar wakilan Amurka cewa akwai yiwuwar ko kuma yana fatar za'a yi taron kolin kamar yadda aka shirya.

A halin da ake ciki kuma, jiya Laraba kwamitin sulhu a Majalisar Dinkin Duniya ya amincewa tawagar wakilan Korea ta Arewa zuwa kasar Singapore domin halartar taron kolin da ake son yi tsakanin Amurka da Korea ta Arewan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG