Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin a Ina Trump Da Kim Jong Un Za Su Yi Taronsu?


Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un
Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un

Fadar gwamnatin Amurka ta White House, ta ce nan da kwanaki uku masu zuwa za'a bayyana inda shugaban Amurka da takwaran aikinsa na Korea ta Arewa za su yi taronsu.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce nan da kwanaki uku masu zuwa za a sanar da wuri da ranar da za a gudanar da taron koli tsakaninsa da shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un.

Amma bayanai sun yi nuni da cewa ba za a gudanar da taron a yankin Korea ba da aka hana ayyukan soji kamar yadda aka fada a baya ba.

Trump ya yi wadannan kalamai ne ga manema labarai a fadarsa ta White House, jim kadan bayan Korea ta Arewa ta sako wasu Amurkawa uku da take tsare da su.

Mujallar Wall Street Journal ta fada da yammacin jiya Laraba cewa akwai yiwuwar a gudanar da taron kolin a kasar Singapore.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG