Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron kolin kasashen Afrika


Kasashen Afrika zasu aika da karin sojoji zuwa Somalia.

Shugabannin Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka (AU) sun yanke shawarar tura karin sojoji 2,000 zuwa Somaliya, inda masu tsattsauran ra’ayin Islama ke kokarin kifar da gwamnatin. An cimma shawarar ce a wajen taron kwannaki ukku na shuwagabannin Afrika din da aka yi yau Talata a Uganda. Idan aka cika alkawarin tura karin sojojin to yawan sojojin tabbatar da zaman lafiya a Somaliya zai kai 8,000 ke nan. Dakarun da suke wurin a halin yanzu sun fito ne daga Uganda da Burundi, to amman shugaban babban Kwamitin zartaswa na AU Jean Ping, yace kasar Guinea ma na shirin tura wasu dakarunta. Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Johnnie Carson ya gana da shugabanni da dama na kudanci da gabashin Afirka ranar Litini. Yace sun dukufa ga karfafa dakarunsu don karya lagon al-Shabab—watau kungiyar nan mai anfani da makamai da ke kokarin mai da kasar Somaliya mai tsattasuran bin tsarin Islama.

XS
SM
MD
LG