Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da a gaggauta yin zab’e


Majalisar dattawan Najeriya ta zartas da gyaran kundin tsarin mulkin da zai maida yin zab’e a cikin watan janairu, wato watanni ukku kafin lokacin da aka saba yi.

Gaggauta yin zab’en zai yi matsin lamba ga jam’iyyar da ke mulkin kasar yanzu ta warware husumar cikin gidan da ake yi akan ko ta yarda da takarar shugaba mai ci yanzu Goodluck Jonathan dan kudancin k’asar ko kuma ta nemi wani d’an takara na daban daga arewacin k’asar.

Amma har yanzu dai gyaran kundin tsarin mulkin na buk’atar amincewar majalisar wakilan k’asar. Gyaran na neman a yi zab’e ne cikin kwanaki 120 zuwa kwanaki 150, wato cikin watanni hud’u zuwa biyar kafin sabon shugaban da za a zab’a ya fara wa’adin mulkin shi a cikin watan mayu.

Yin hakan zai bada k’arin lokacin warware duk wata gardamar zab’en da ta kai kotu kafin sabon shugaba ya kama aiki. Amma kuma ta wani gefe yin hakan zai kawo rashin isasshen lokacin yin shirye-shiryen zab’e, kamar yin rajistar masu zab’e cikin nagarta da inganci, kuma hakan zai sa shugaba Jonathan ya hanzarta fitar da tsarin abubuwan da zai yi, ko da yake dai har yanzu bai ce uffan ba game da ko zai tsaya takara ko kuma a’a.

An yi wata da watanni ana jayayya akan zab’en k’arshen da aka yi a Najeriya a shekarar dubu biyu da 7, jayayyar da aka ci gaba da yi har ma bayan marigayi shugaba Umaru Musa ‘Yaradua ya kama aiki.

Wasu ‘yan jam’iyyar PDP mai mulkin kasar sun ce ya kamata d’an takara ya fito daga arewa tun da marigayi shugaba ‘Yaradua d’an arewa ne kuma Allah bai bashi ikon kammala wa’adin shi ba. Jam’iyyar ta PDP mai mulki ita ce ke bin tsarin yin shugabancin karb’a-karb’a tsakanin kudu da arewa.

XS
SM
MD
LG