Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Kwamitin Ciyar da Najeriya da Shinkafa da Alkama


Taron kwamitin yawalta shinkafa da alkama. Daga hagu zuwa dama: Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi, Umar Ganduje na Kano, David Omahi na Ebonyi, Badaru Abubakar na Jigawa da Farfasa Yemi Osinbajo, Mukaddashin shugaban Najeriya

Kwamitin da aka kafa na ciyar da Najeriya da shinkafa da alkama yayi taro da Mukaddashin Shugaban Najeriya Farfasa Yemi Osinbajo a fadar shugaban kasa dake Abuja.

A taron mukaddashin shugaban kasa yayi farin ciki da kwazon da jihohi su keyi wajen kara yawan noman alkama da shinkafa.

Farfasa Yemi Osinbajo ya bada tabbacin za'a cigaba da taimaka ma manoma da masu sarrafawa da masu dauka su kai wurare daban daban domin a samu yalwa da samun wadatar shinkafa da alkama a koina cikin fadin kasar Najeriya.

Inji Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi abubuwa biyu ne ke faruwa. Yace Allah Ya albarkaci wannan tsarin noma da ake yi.Ya kara sa duk nahiyar yammacin Afirka daga Najeriya ake sayen shinkafa da alkama. Yace tunda ana saye daga kasar to idan ko an kara nomawa za'a ragewa masu zuwa kasuwa neman shinkafa da alkama.

Bugu da kari Shugaban kasa Muhammad Buhari ya sake jaddada burinsa na ganin manomi ya samu arziki daga noman da yake yi, manomi ya samu yalwa. Saboda haka idan mutum yana sha'awar kada ya saya shi ma sai ya je ya noma.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:36 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG