Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Majalisar Dinkin Duniya Akan Zaman Lafiyar Syria


Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry

Babban jami’in diflomasiyyar Amurka yace, shirin tattaunawar zaman lafiyar majalisar dinkin duniya game da rikicin kasar Syria zai ci fara a ranar Litinin mai zuwa kamar yadda aka tsara.

Duk kuwa da zargin saba yarjejeniyar daga bangaren gwamantin Syria. Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya bayyana cewa, masu sa ido daga Rasha da Amurka suna taro a biranen Geneva da Amman tun daga jiya Asabar, domin neman mafitar yadda za a kawo saukin rikicin Syria.

Kerry ya fada a Saudiyya cewa, daga bayanan da ake samu, rikicin na Syria ya rago da akalla kaso 80 zuwa 90, wanda hakan na da matukar muhimmanci in ji Sakataren wajen Amurkan.

Ministan harkokin wajen Syria Walid Muallem yace gwamnatinsu zata yi iya kokarinta kiyaye dokar tsagaita wuta amma ya nemi masu shiga tsakanin da su kara kwana 1 don jira isowar wakilan ‘yan adawa.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG