Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Masu Hannu Da Shuni Da Manoman Albasa A Nijar

A watan Disambar bara ne Shugaban Nijar Mahammadou Issoufou ya jagoranci wakilan kungiyar masu noman albasa zuwa kasar Faransa domin neman masu hannu da shuni su saka jari

Karshen makon jiya hakkan manoman albasa a Jamhuriyar Nijar ya cimma ruwa domin ko masu hannu da shuni daga Faransa sun cika alkawarinsu sun ziyarci jihar Toua, jihar da aka fi noma albasa a duk fadin Nijar.
Tawagar ta himmatu kuma ta tabbatar zata kafa injin nika albasa a jihar wanda zai sa a daina fitar da alabasar danya daga kasar. Hakan kuma zai yi maganin rubewarta a kasar da zummar habaka arzikin da manoman zasu dinga samu.

Domin Kari

XS
SM
MD
LG