Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Nazarin Nasarorin Jami’an Tsaron Najeriya Na Wannan Shekara


Taron Nazarin Nasarorin Jami’an Tsaron Najeriya Na Wannan Shekara
Taron Nazarin Nasarorin Jami’an Tsaron Najeriya Na Wannan Shekara

Yayin da jama'a har yanzu ke fama da rashin tsaro a Najeriya, gwamnatin kasar ta ce ta na samun galaba wajen yaki da yan ta'adda, kuma ta na kusa da bude sashen kula da sauka da tashin Jiragen sama na rundunar sojin kasa.

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ta'allaka nasarar da ya ce ana samu ga gagarumin shirin samar da kayan aiki na zamani ga mayakan kasar.

Najeriya ta kwashe shekaru cikin halin rashin tsaro wanda yayi sanadiyar salwantar rayukan jama'a da dukiyoyin jama'a da dama, wanda gwamnatin kasar ta dade tana fafatukar magancewa.

Sai dai shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce gwamnatin sa ta yi rawar gani wajen karya lagon ‘yan ta'addar, kuma ta na kan kokarin magance matsalolin ta hanyar samar da ingatattun kayan aiki na zamani ga mayakan kasar.

Ya ce “za'a yi shiri na musamman domin bude sashen kula tashi da saukar jiragen sama na rundunar sojin kasa, inda ya ce anyi tanadi a cikin kasafin kudin 2023 domin hakan.”

Taron Nazarin Nasarorin Jami’an Tsaron Najeriya Na Wannan Shekara
Taron Nazarin Nasarorin Jami’an Tsaron Najeriya Na Wannan Shekara

Yanzu haka dai akwai mayakan kasar da ke fafatawa da ‘yan ta'adda a karkashin shirye-shirye masu yawa wadanda babban hafsan mayakan kasar Lt. Gen Faruk Yahaya, ya ce kwalliya na biyan kudin sabulu saboda ingatattun shirin samar da kayan aiki da inganta jin dadin jami'an sojin.

Ya ce “hakan ya kara kuzarin jami'an soji dake fafatawa a wurare da daban daban, haka ma kyakkyawar huldar aiki da wasu hukumomi ya taimaka gaya, za'a ci gaba da horas da jami'an tare da kula da sauyin jami'an da suka jima fagen daga suna fafatawa domin a tura sabbin jini"

Yanzu haka dai kumandojin mayakan na Najeriya na kan bitar ayukkan da suka gabatar a wannan shekara, tare da sake kimtsawa da kara shirin fita fagen daga domin samar da tsaron kasa, abin da wasu ke fatan ganin an samu nasara.

Taron Nazarin Nasarorin Jami’an Tsaron Najeriya Na Wannan Shekara
Taron Nazarin Nasarorin Jami’an Tsaron Najeriya Na Wannan Shekara

Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan aikin soji Sanata Ali Ndume ya ce akwai fatar ganin an samu nasara ga ayukkan sojin musamman jin irin kalaman da shugaban kasa ya yi da kuma bude sashen kula da jiragen sama na rundunar sojin kasa.

Duba da har yanzu matsalar tana wanzuwa duk da wadannan tarin nasarori da ke bayyana ana samu, masanin tsaro kuma tsohon babban hafsan mayakan Najeriya Lt. Gen. Tukur Yusuf Buratai, wanda rundunar sojin ta karrama tare da wasu mutane biyar ya ce lamarin samar da tsaro ba abu ne da za'a iya yi kai tsaye ba dole sai anyi hakuri, kuma kowa na da gudunmuwar bayarwa ga samun nasarar sa.

Saurari rahotan Muhammad Nasir cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

XS
SM
MD
LG