Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Sauyin Yanayi: Farfado Da Martabar Yanayin Duniya


Shugaba Emmanuel Macron
Shugaba Emmanuel Macron

Yanzu Shugaban Faransa Emmanuel Macron ke jan ragamar yaki da matsalolin sauyin yanayi inda ya tattaro manyan 'yan kasuwa da shugabannin duniya 50 a wani taro a Paris yau talata wanda zai mai da hankali kan habbaka daukan nauyin kawar da sauyin yanayi.

Taron ya zo bayan kusan shekaru biyu da kasashe dari biyu suka cimma yarjejeniyar kare yanayi ta Paris, wadda ta bukaci kasashe su takaita iskar gas mai dumama yanayi da suke fitarwa, yayin da su kuma kasashe masu arziki zasu taimakawa kananan kasashe ta yadda zasu iya shawo kan matsalolin sauyin yanayi.

Ba a gayyaci shugaba Donald Trump na Amurka zuwa wurin wannan taron ba. A shekarar da ta shige, shugaban na Amurka ya bayyana janye hannun kasarsa daga wannan yarjejeniya, yana mai cewa tana takura ma Amurka yayin da take dadada ma wasu kasashen.
sauran kasahe.

Yayin da gwamnatin tarayya a Amurka ta janye hannunta daga wannan yarjejeniya, gwamnatocin jihohi da na manyan birane da dama sun yi alkawarin ci gaba da daukar matakai irin wadanda aka zayyana su karkashin wannan yarjejeniya.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG