Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Shugabannin Fulani Makiyaya a Jihar Taraba


Fulani makiyayi.

Yayin da ake fama da matsalar satar shanu da kuma garkuwa da mutane a jihar Taraba, matsalar da yanzu ke neman hana jama’a barci a jihar, shugabanin Fulani makiyaya sun gudanar da wani taron nemo bakin zaren magance wadannan matsaloli da akan dangantawa da makiyaya.

Jihar Taraba na cikin jihohin dake fama da matsalar inda wasu yan bindiga kan bi dare suna satar shanu, tare da garkuwa da jama’a domin neman kudin fansa.

Wasu shugabanin makiyaya a jihar Taraba, da suka halarci wannan taro na gano bakin zaren magance matsalar satar shanu da kuma garkuwa da yayan makiyaya domin neman kudin fansa, lamarin dake hana al’umma barci a jihar Taraba.

Shi dai wannan taro da aka gudanar a Iware, dake zama daya daga cikin cibiyoyin kasuwanin shanu a Taraba, ya hada hancin shugabanin kungiyoyin makiyaya daga ciki da wajen jihar, da zimmar lalubo bakin zaren magance wadannan matsaloli.

Shi ma Ardo Hussaini Yusuf Bosso, dake zama mataimakin shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah a Najeriya, ya yabawa jihar Taraba, bisa wannan yunkuri.

Kamar yadda alkalumman hukumomin tsaro ke nunawa, a yan watannin nan barayin shanu a jihar sun sace daruruwan shanu, yayin da aka gano wasu kuma har yanzu kake ji kamar an shuka dusa baya ma ga batun garkuwa da makiyayan da ake ci gaba da yi.

Ko da yake hukumomin tsaro a jihar kullum cewa suke suna kokari. CP Yakubu Yunana Babas, shine kwamishinan yan sandan jihar. Yace ‘’ai ba’a kwance muke ba, domin kullum jami’an mu na cikin shirin ko ta kwana, alal misali ko a yan kwanakin nan, ai sai da aka gano wasu shanu kuma yanzu haka muna bincike don mai da su ga masu su. Mu dai hadin kai muke nema don magance wadannan matsaloli na satar shanu dama garkuwa da mutanen, kasan akwai hanyoyin bincike da muka dakile ayyukan bata garo da muke bi a yanzu.’’

XS
SM
MD
LG