Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Sufuri a Najeriya


Babur din “A Dai Dai Ta Sahu” ya kasance hanyar da aka fi amfani da shi wajen sufuri a birnin Kano, amma matukansa basu damu da bin dokokin titi ba. Yuni 10, 2013.

Yau aka shirya taron sufuri a Najeriya

An fara taron sufuri a Najeriya inda kowace jiha ta samu wakilci.

Taron na kwana hudu an shirya shi ne domin samo hanyar da za'a inganta sufuri a duk fadin Njeriya. Ana taron ne a birnin Legas. Taron ya taro masaa kan harkokin sufuri daga sassa daban daban na kasar.

Da yake bude taron babban sakataren ma'aikatar sufuri Inginia Nebosa Imodi ya ce taron shi ne na karo goma sha biyu kuma ya zama wajibi domin ta haka ne ake musayar ra'ayi dangane da yadda za'a iya inganta sufuri a duk fadin kasar. Ya ce babu shakka sufuri na kan gaba wajen ciyar da al'umma da ma cigaban tattalin arziki gaba daya. Dalilin haka ne ya sa gwamnatin tarayya ta shigo da kamfanoni da wasu cikin wannan taron.

Kwamishanan sufuri na jihar Legas ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta maida hankali kan jihohin dake fama da cinkoson jama'a wajen sufuri domin sufuri yana cikin abun da ke sa cigaban al'umma.

Ga Ladan Ibrahim Ayawa da rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:07 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG