Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Zaman Lafiya Tsakanin Falasdinawa Da Isra'ilawa


Kasar Bahrain da Amurka sun fada a jiya Lahadi cewa zasu shirya taro mai taken zaman lafiya zuwa ga ci gaba a cikin watan Yuni domin farfado da harkokin tattalin arziki Falasdinu, indai har za a cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Falasdinawa da Isra’ila.

Fadar White House tayi alkawarin fitar da sabon tsarin taron zaman lafiya a makwanni biyu masu zuwa, wanda Jared Kushner surikin shugaba Donald Trump kuma mai bada shawara a fadar White House ya shirya wani bangare.

Isra’ila da Falasdinawa sun gaza cimman yarjejeniyoyin zaman lafiya da aka kula shekara da shekaru, amma tsarin Amurka ya yi tanadi inganta tattalin arziki a cikin sabon tsarin zaman lafiya a taron tattalin arzikin a Manama babban birnin kasar Bahrain, a ranakun 25 da 26 na watan Yuni.

Wani babban jami’in fadar White House ya fada a jiya Lahadi cewa, sabon tsarin ya yi kira ga zuba jari a harkokin tattalin arzikin Gaza, amma kuma zuba jarin zai bukaci a tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya da tsagaita wuta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG