Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Hari Ta Sama A Afghanistan Ya Hallaka Mutane Da Yawa


Wani harin sojan jiragen sama na kasashen waje da aka kai kudancin lardin Helmand dake Afghanistan, ya kashe mutane akalla 17 a bisa kuskure, tare da kuma raunata wasu 14.

A yau Jumma’a wani jami'in tsaron yankin, wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya shaidawa gidan rediyon Muryar Amurka yawan mutanen da suka mutu, inda yace, harin ya faru ne a babban birnin lardin Lashkar Gah, inda 'yan sanda ke gwagwarmaya da 'yan kungiyar Taliban.

Tun a farko a wata sanarwa da ta bada, ma’aikatar harakokin cikin gidan Afghanistan, ta ce artabun da aka yi yayi sanadin mutuwar ‘yan sanda 11 ya kuma raunata wasu 11.

Ma’aikatar ta kara da cewa rundunar sojan kasa da kasa da Amurka ke jagoranta ne suka kai harin a bisa bukatar gwanmatin Afghanistan da ta nemi taimakonsu wajen yakar ‘yan ta’adar Taliban a gundumar Nahre-Saraj.

Har ya zuwa yanzu dai rundunar gamayyar sojojin na kasa-da-kasa bata amsa bukatar da gidan radiyon nan na VOA yayi musu ba don su maida martini ga wannan rahoton.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG