Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin Bamabamai a Murikalmari Kusa da Maiduguri Ya Kashe Mutane


Harin kunar bakin wake a Murikalmari, Maiduguri

Harin kunar bakin wake da wasu mata hudu suka yi a daren jiya a Murikalmari dake dap da Maiduguri yayi sanadiyar mutuwar mutane 19 tare da jikata wasu 23

Rundunar 'yansandan jihar Borno ta tabbatar da mutuwar wasu mutane 19 da kuma wasu 23 da suka samu munanan raunuka sakamakon tashin wasu bamabamai da ya auku a daren jiya a kauyen Murikalmari dake kusa da Maiduguri.

Tun a daren jiya ne mazauna yankin suka ce suna jin karan tashin bamabaman da suka auku a wurare daban daban har guda hudu.Wadanda suka tada bamabaman 'yan kunar bakin wake ne mata yayinda suka dinga afkawa cikin jama'a da misalin karfe goma da wasu 'yan mintuna.

'Yan jarida da suka hada da wakilin Muryar Amurka sun ziyarci inda lamarin ya faru da safiyar yau. Mutane da dama suka dinga yi masu bayanin abun da ya auku.

Kwamishanan 'yansandan jihar Borno Mr. Daniel Chukwu wanda ya halarci kauyen yayi karin haske. Yana mai cewa 'yan kunar bakin waken hudu ne. Dayarsu ta auna kai hari akan 'yan kato da gora ko 'Civilian JTF' kafin kuma a ankara ta tayar da bam din dake jikinta inda nan take mutane shida suka sheka lahira wasu kuma suka ji raunuka.

Wata kuma ta shiga gidan da ake ta'aziyar wani da Allah ya yiwa rasuwa nan kuma ta tayar da bam din dake jikinta ta kashe mutane 11 tare da ita kanta. A wurin da ake kira Sabon Garin Mulai nan ma wasu sun mutu.

Yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutane 19 da kuma 23 da suka samu munanan raunuka. Cikin mutane 19 da suka mutu 12 'yan "Civilian JTF" ne.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG