Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tasirin Sintirin Da Sojojin Najeriya Ke Yi a Sassan Kasar


Zaratan sojojin Najeriya a garin Gudumbali dake Jihar Borno a bayan an kwato garin. An samu hoton bayan da zaratan sojojin Najeriya suka sake fatattakar 'yan Boko Haram daga garin dake Jihar Borno

A Najeriya sojojin kasar da dama na jibge a wasu yankuna domin gudanar da sintiri da atisaye, musamman domin kwantar da hankulan jama'a da kuma wanzar da zaman lafiya. Shin mene ne tasirin irin wannan sintiri?

A sassa daban daban na Najeriya dakarun kasar kan gudanar da atisaye na musamman inda akan jibge su su yi kwana da kwanaki ko kuma su dauki wani tsawon lokaci suna atisayen.

Akan kai dakarun ne yankunan da ke fama da wasu matsaloli na musamman, misali a yankin da ake fama da matsalar satar shanu ko tsagerun yankin Niger Delta ko masu fashi da makami ko satar mutane.

Sannan akan shirya irin wannan atisaye har ila yau a yankunan da ake fama da matsanancin rashin tsaro kamar na Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya, da kuma matsalar ‘yan aware ta ‘yan kungiyar IPOB da ke kudu maso gabashin kasar.

Har ila yau akan aike da dakaru, saboda yankunan da ke fama da rikicin kabilanci ko na addini.

Daga cikin ire-iren wadannan sintiri, akwai “Operation Lafiya Dole” da “Operation Crack Down” da “Operatino Gama Aiki” da “Operation Safe Corridor” da “Operation Safe Haven” da “Operation Sharar Daji” da “Operation A Watse” da dai sauransu.

Amma shin wanne irin tasiri ire-iren wadannan sintiri ke yi a sassan Najeriya, ku saurari rahoton Hassan Maina Kaina:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG