Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tasirin Zaben Alabama Kan Makomar Trump


Alabama Special Election

Masu jefa kuri’a a Jihar Alabama a nan Amurka suna zaben cike gurbin wata kujerar majalisar dattijan tarayya da kowa ya sanya idanu a kai, domin cike gurbin da Jeff Sessions ya bari lokacin da ya zamo atoni janar.

Ana wannan takara ne a tsakanin Roy Moore na jam’iyyar Republican, mutumin da ake cacar baki sosai a kan ra’ayoyi da dabi’unsa, da kuma dan takarar Democrat, Doug Jones, wanda tsohon mai gabatar da kararraki ne.

Sakamakon wannan zaben zai iya dora tasiri a kan makomar shugaba Donald Trump da kuma martabar dukkan jam’iyyun nan biyu.

Moore ya musanta zarge zarge da dama da aka yi masa na lalata ko neman lalata da kananan yara mata, ciki har da wata mai shekara 14 a lokacin yana da shekara talatin da wani abu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG