Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattalin Arzikin Kasashe Da Dama Zasu Farfado A Afirka


Neft və dollar

Kamar yadda aka yi hasashe shekara ta dubu biyu da goma sha shidda ta sa tattalin arzikin kasashen Afrika dandanawa.

Kasashe Najeriya da Afrika ta kudu sun yi fama da matsalar komadar tattalin arziki yayinda suma wasu kasashe suka dandana a saboda faduwar farashin mai a kasuwanin duniya.

Masana tattalin arziki sunyi hasashen cewa, kasashen Afrika ta dama zasu dan farfado a shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai, to amma akwai bukata ga kasashen Afrika ta dama su kara zage dantse.

Najeriya, tayi fama da hauhawan farashin kayayyaki wanda rabon da taga irin haka tun shekaru goma sha daya da suka shige.

Sai kuma Afrika ta kudu data samu karuwar zaman dar dar a saboda abun fallasar data shafi shugaba Jacob Zuma na kasar.

Komadar tattalin arziki ta taka rawa ga kayen da shugaban Ghana John Dramani ya sha a zaben shugaban kasar da aka yi.

To amma kuma masana suna hasashen cewa idan Allah ya yarda a shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai za’a ga ingantuwar al’amurra.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG