Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattaunawa da Koriya ta Arewa Bata Lokaci Ne, Inji Shugaban Amurka, Trump


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump yace kokarin tattaunawa da shugaban Koriya ta Arewa da sakataren harkokin wajen kasarsa keyi bata lokaci ne kawai.

A wani abu mai kama da tarar numfashin babban jami'in diflomasiyyar gwamnatinsa a jiya Lahadi, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson na abin da ya kira, "bata lokacinsa ne kawai" wajen kokarin tattaunawa da Shugaban Koriya Ta Arewa.

A wasu jerin sakonnin twitter, Shugaban na Amurka ya ce: "Ka daina wahal da kanka Rex, za mu yi abin da ya zama dole"

'Yan sa'o'i kadan bayan aika wannan sakon, sai Trump ya yi karin haske da cewa "rangwantawa da lallashin "Dan Rokar Koriya" da aka shafe shekaru 25 ana yi bai yi alfanu ba, ta yaya zai yi a yanzu? Clinton ya kasa, Bush ya kasa kuma Obama ya kasa. Amma ni kam ba zan kasa ba."

Koriya Ta Arewa ta bayyana baro-baro cewa ta na daukar lakabin "Mai-Roka" da Trump ya yi ma Kim Jong Un, wanda ya gaji mahaifinsa Kim Jong il bayan mutuwarsa a 2011, a matsayin zagi.

A yayin da Shugaba Trump ke aikawa da sakonnin na twitter, wata mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Heather Nauert, ta fadi ta kafar twitter cewa Koriya Ta Arewa, "ba za ta taba mallakar fasahar nukiliya ba, kuma ko hakan zai kasance ne ta hanyar diflomasiyya ko da karfi da yaji, ya rage ga gwamnatin."

Tillerson dai, yayin da ya ke birnin Beijing kwana guda kafin nan, ya fada cewa Amurka na da kafar diflomasiyya ta kai tsaye ta tattaunawa da Koriya Ta Arewa kan batun cigaba da gwaje-gwajenta na nukiliya da makamai masu linzami.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG