Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattaunawar Zaman Lafiyar Syria Ta Samu Nasara A Diflomasiyance


Shugabannin taron zaman lafiyar Syria

Firayim Ministan Turkiyya Binali Yildirim ya fadi jiya Labara cewa tattaunawar zaman lafiyar Siriya da ake yi a wannan satin a Kazakhstan, ta zama wata babbar nasara a diflomasiyyance.

Turkiyya da Rasha da Iran sun taimaka wajen shirya tattaunawar ta tsawon kwanaki biyu a Astana tsakanin wakilan gwamnati da kuma na 'yan tawaye, inda a karshe su ka amince cewa za su saka ido kan takaitacciyar tsagaita wuta a Siriya su kuma ba da goyon baya ga kokarin da ake yi na samo mafita a siyasance a wannan tashin hankalin da kasar ke fama da shi.

Yildirim ya ce ya kamata mafitar ta hada da kafa sabuwar gwamnati a Siriya wadda za ta yi tafiya da dukkannin bangarorin.

Wani batu mai sarkakkiya a tattaunawar zaman lafiyar da aka yi ta yi a baya shi ne irin rawar da Shugaba Bashar al-Assad zai taka a sabuwar gwamnatin. 'Yan tawayen na so ya sauka daga mulki, to amma magoya bayansa ciki har da Rasha, na so ya cigaba da mulki.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG