Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Ministan Watsa Labaran Najeriya Ta Gana da Shugaba Buhari a London


Shugaba Muhammad Buhari

Tawagar Ministan Watsa labaran Najeriya Lai Muhammad ta gana da Shugaba Muhammad Buhari a London , sun tattauna dashi sun dauki hotuna da bidiyo

A karon farko 'yan Najeriya sun ga hoton bidiyo na shugaba Muhammad Buhari yayinda tawagar ministan watsa labaran Najeriya Lai Muhammad ta isa wurinsa a birnin London.

Hoton ya nuna shugaban yana raha da ganawa da karanta wasu katuna da aka kai masa har ma sun fita waje daga cikin gidan inda suka kara yin hotuna.

Malam Garba Shehu mai taimakawa shugaban akan harkokin 'yan jarida yana cikin wadanda suka gana da shugaban ya kuma yi karin bayani.

Yana mai cewa sun godewa Allah da suka samu suka ganshi domin duk abun da suka sani da daga rahotannin da abokan aiki ke aika masu ne. Amma wannan zuwan sun ganshi sun ji muryarsa yana raha da mutane kuma 'yan Najeriya sun ga hotunan tare da jin muryarsa ta kafar talibijan.

Acewar Garba Shehu shugaban yace idan don ta shi ce bai ki ya tashi ya koma Njeriya ba nan da nan amma hakan ba zai yiwu ba sai da amincewar likitocinsa.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG