Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Pence Za Ta Turkiyya Don Matsa Lamba Ma Shugaban Kasar


Mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence, zai jagoranci wata babbar tawaga zuwa Turkiyya, domin nuna matsin lamba ga shugaba Recep Tayyib Erdogan kan ya kawo karshen mamaye arewacin gabashin Syria da ya yi.

Shugaban Amurka Donald Trump ne ya bayyana shirin wannan ziyara da tawagar za ta kai a yau Laraba, wacce ya ce za ta kunshi har da Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, da nufin yin kira ga Turkiyyan da ta tsagaita wuta, yana mai cewa, akwai tsauraran matakai da Amurkan za ta dauka akan Turkiyyan idan ba ta mika wuya ba, ciki har da matakin saka makudan kudaden haraji kan kayayyakin karafa da Turkiyyar ke shiga da su Amurka.

Tun bayan da ya ba da umurnin kaddamar da mamayar, Shugaba Erdogan, ya yi biris da kiraye-kirayen da kasashen duniya suke mai na ya janye dakarunsa, yana mai kafa hujja da cewa, so suke su kawar da duk ‘yan ta’addan da suke kan iyakar kasarsa da Syria, abin da ya ce suna samun nasarar.

Erdogan yayi bayani cikin harshen Turkanci, inda yake cewa, “mun kawar da duk ‘yan ta’addan da ke garin Jarabulus, shin Turkawa sun yi kama-wuri-zauna a garin? A’a, ‘yan asalin garin ne kawai a wurin.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG