Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ted Cruz na jam'iyyar Republican ya zabi Fiorina a matsayin mataimakiyarsa


Carly Fiorina da Ted Cruz
Carly Fiorina da Ted Cruz

Daya daga cikin masu neman jam’iyyar Republican ta tsayar da shi dan takararta na neman shugabancin Amurka Ted Cruz, ya zabo tsohuwar jami’ar wani kamfanin na’ura mai kwakwalwa kuma tsohuwar ‘yar takara Carly Fiorina a matsayin mataimakiyar Shugaban Kasa in yaci zabe.

Fiorina ta taba shugabantar kamfanin Kwamfutar nan na Hewlett Packard ko HP a takaice, wadda daga baya aka tunbuketa daga mukamin bayan wani sake lalen da kamfanin yayi.

Ta taba tsayawa takarar neman jam’iyyar Republican ta tsayar da ita a matsayin ‘yar takara, ta kuma halarci muhawarorin neman shugabancin, inda daga baya ta janye bayan ta dan yi tasiri a watan Fabrairun da ya wuce.

Fiorina tace, ta yi matukar farin ciki da alfaharin wannan zabowar da Ted ya yi mata, a matsayin wacce zasu tafi tare a matsayin mataimakiyarsa idan ya kai ga lashe zaben takarar Shugabancin Amurka.

Ba kasafai dai ‘yan takarar neman shugabancin Amurka ke fadar wanda za su dauka a matsayin mataimaki ba idan sun ci zabe, sai gashi kwatsam Ted Cruz ya sanar da ita a matsayin wacce zata zama mataimakiyarsa.

Ted dai ya lashi takobin ganin ya yi duk mai yiwuwa wajen takawa dan takarar da ke sahun gaba na jam’iyyar ta Republican wato Donald Trump burki, na ganin bai zama wanda jam’iyyar taso zata tsayar a matsayin dan takararta ba a gangamin jam’iyyar da za ayi a watan Yuli mai zuwa.

XS
SM
MD
LG