Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cruz Ya Doke Donald Trump Ya Samu Kashi 48 Shi Kuwa Trump Ya Samu Kashi 35


Sai dai dan takarar Republican Donald Trump bai ce uffan ba game da wannan nasarar ta Cruz

‘Yan takarar shugaban kasa a zaben fidda gwani da akeyi na Amurka, Dan takaran jamiyyar Republican Ted Cruz da takwaran sa na jamiyyar Democrat Bernie Sanders suna biye kud da kud ga abokan karawar su dake gaban su a cikin jamiyyun tasu domin ganin sun samu nasarar.

Domin ko kowannen su ya samu nasara na azo a gani a zaben da aka yi jiya talata a arewacin jihar Winscosin.

Cruz dai ya doke Donald Trump inda ya samu kashi 48, shi kuma Trump din ya samu kashi 35, Inda ya kira wannan nasarar a wata babban abu mai muhimmaci ga Amurkawa, daga nan kuma sai ya koma ta kan takwarar sa ta jamiyyar Democrat dake kan gaba a wannan zaben yana cewa ba a cikin jamiyyar su kadai zai samu nasara ba a’a har ma ga wanda ya tsaya takara a jamiyyar Democrat a zaben gama gari da za a yi a cikin watan Nuwamba.

Cruz yace domin haka Hilary ta kwana cikin shiri domin ko ita ta gaba wadda zai kayar.

Sai dai dan takarar Republican Donald Trump bai ce uffan ba game da wannan nasarar ta Cruz, sai dai kungiyar kanfe dinsa ce ta fitar da sanarwan dake sukar Cruza matsayin wanda wasu keson suyi anfani

XS
SM
MD
LG