Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TEXAS: An Kori Dansandan da Ya Kashe Wani Dalibi


Dansanda Brad Miller da ya kashe Christian Taylor wani dalibi.
Dansanda Brad Miller da ya kashe Christian Taylor wani dalibi.

Yanzu haka an kori dan sandan nan na birnin Dalas bakin aiki,wanda ke cikin jihar Texass sakamakon harbin wani dan makaranta bakar fata kuma ya kashe shi.

Babban jamiin yan sanda Will Johnson dake yankin Arlington ya bayyana jiya talata cewa an kori Brad Miller daga bakin aiki bayan samun sa da laifin harbin wani dalibi dan shekaru 19 Christian Taylor, wanda mutuwar sa ta haifar da tarzoma da rashin kwanciyar hankali a yanbkin su.

Shi dai Miller wanda ya shiga aikin dan sanda kasa da shekara guda zuwa lokacida ya aikata wannan danyen aikin, ya yi kokarin hana sata ne da ake tuhumar shi marigayi da aikatawa a shagon masu sayar da motoci a ranar wata jumaa.

Miller wanda ya hango Talor cikin wannan shagon maimakon ya agaza domin shi da sauran yan sanda yan uwanshi a kauce wa aikata wannan sa in sa tsakanin sa da da wanda ake tuhunma maimako sai saitinkare shi shi kadai.

Jonhson yace sailin da Taloy yaki bin umurnin Miller , kawai sai ya bude masa wuta ya harbe shi har sau 4.

Shugaban yan sandan yace Miller na iya huskantar hukunci aikata ayyukan assha yace sai dai ba a cimma matsaya ba akan hakan ba tukunna

XS
SM
MD
LG