Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

THAILAND: Mahukunta Na Neman Wadanda Suka Tayarda Bamabamai


Wurin da aka kai hare-hare

Firayim ministan kasar Thailand Prayuth Chan-ocha yace jami’ai na cigaba da binciken wasu mutane yau Talata, wadanda aka gani ta kyamar sanya idanu a inda wata fashewa ta auku a babban birnin kasar lamarin da yayi sanadiyar rayukan a kalla mutane 22, wasu 120 suka raunata.

Shugaban ya bayyana cewa akwai mutanen dake kokarin lalata kasar saboda dalilai da dama.

Yace “kokarin da ake cigaba da yi na barna, ta iya yiwuwa na da nasaba da siyasa, saboda farmakin da ake kaiwa tattalin arzikin kasa, da harkokin yawon bude idanu, ko kuma ma wasu dalilai”, a cewar Ministan a lokacin da yayi jawabi har aka watsa a gidajen talabijin. Yace gwamnati zata cigaba da binciken wadannan mutane, sannan zata ta tabbatar da shari’a a kan su nan bada jimawa ba.

Daya daga cikin mutanen da jami’ai suka ce suna zargi, an gan shi ne a kyamarar sanya idanu da aka fi sani da CCTV jim kadan kafin fashewar jiya Litinin. A wasu hotunan bidiyo da aka fitar yau Talata, an ga wani mutum ya sauke wata jaka daga bayan sa akan wani benci, sannan ya yi tafiyar sa. Jami’ai sun ce fashewar ta auku dakika kalilan bayan sulalewar mutumin.

Duk a jiya Talata an kara samun wata sabuwar fashewa a kusa da wata tasha dake bakin rafi a birnin Bangkok. Jami’an tsaro sun ce an jefa abun fashewar ne daga kan wani gada zuwa cikin ruwa, lamarin ya sa ruwa yayi tsalle sama cikin samaniya, amma babu wanda ya samu rauni.

Fashewar yammacin jiya Litinin a kan titin Rat-cha-pra-song ta faru ne a tsakiyar birnin Bangkok, bakin wani wajen ibada. Wadanda suka rasu sakamakon wannan fashewa a cikin su akwai ‘yan asalin Thailand 6, da mutan Malaysia 4, da ‘yan Chana guda 3. Hakan ya nuna farin jinin wannan wajen ibada a nahiyar Asiya.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG