Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tiger Woods Ya Yi Mummunan Hatsarin Mota


Tiger Woods

Fitacce dan wasan kwallon golf din Amurka Tiger Woods ya yi wani mummunan hatsari a cewar ofishin ‘yan sandan birnin Los Angeles.

Rahotanni sun ce motar Woods ta wuntsula ne a kusa da wani yanki da ake kira Ranchos Palos Verde a jihar California, lamarin da ya sa sai da aka zakulo shi daga cikin motar da gabanta ya malkwade.

Wani hotan bidiyo da ya nuna inda hatsarin ya faru, ya nuna motar jirkice a kasan wani rami da ke gefen tsauni, an kuma ga wasu sassan motar a warwatse a inda motar ta fadi.

An dai garzaya da Woods asibitin Harbor- na UCLA, inda “ake yi masa maganin raunukan da ya ji yayin da bayanai ke nuna cewa shi kadai ne a cikin motar a lokacin da hatsarin ya auku.

Motar da Tiger Woods ya hatsari (KNBC via Reuters)
Motar da Tiger Woods ya hatsari (KNBC via Reuters)

“Tiger Woods na cikin wata mota shi kadai a wannan safiya a California inda ya samu raunuka da dama a kafa.” Wani hadimin Woods, Mark Steinberg ya ce.

Dan shekara 45, Woods ya je yankin na Los Angeles ne domin halartar wata gasa Golf ta PGA Tour da wata gidauniyarsa ke daukan nauyi.

Woods wanda sau 15 yana lashe manyan gasar golf, bai buga wani wasa ba saboda yana murmurewa daga aikin da aka yi masa a baya a ranar 23 ga watan Disamba.

AFCON 2021, Troost-Ekong

Abin da kyaftin Troost-Ekong ya ce da Najeriya ta lashe wasanninta uku a jere bayan doke Guinea-Bissau
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Super Eagles

Yan wasan Najeriya na atisaye gabanin karawar da za su yi da Guinea-Bissau a rukunkin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021: Troost-Ekong

Kowa ya san cewa mun iya taka leda’ In ji Troost-Ekong, yayin da Najeriya ta kai zagayen knockouts
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG