Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tillerson Na Iya Zama Sakataren Harkokin Wajen Amurka


 Rex Tillerson mutumin da Donald Trump ya zaba a matsayin sakataren harkokin waje
Rex Tillerson mutumin da Donald Trump ya zaba a matsayin sakataren harkokin waje

Senatoci biyu 'yan jam'iyyar Republican masu fada aji, John McCain, da LIndsey Graham, sun bayyana goyon bayansu ga mutumin da Donald Trump ya zaba, ya zama sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson,wanda kamin a zabe shi shine shugaban kamfanin mai na Exon Mobil.

Dangartaka ta kud da kud tsakanin Tillerson da shugaban Rasha Vladimir Putin, yasa Mccain da wasu senatoci sun nuna taraddadi. MCcain, wanda ya bayyana goyon bayansa a cikin wani shirin tashar talabijin ta ABC, yace wannan shawara bata zo masa da sauki ba.

Duk da goyon bayan da McCain da Graham suka bayyana, babu daya daga cikinsu dake kwamitin kula da harkokin kasashen waje, inda ake sa ran kwamitin zai kada kuri'a kan haka a maraicen yau. Senata Marco Rubio na Florida yana kwamitin kuma har yanzu bai bayyana matsayarsa ba.

'Yan Republican suna da rinjaye da senata daya a kwamitin, idan Rubio ya hada kai da 'yan Democrat suna iya kin amincewa da zaben Rex Tillerson daga kwamitin.

XS
SM
MD
LG