Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Kubutar Da Daliban Zamfara


Shugaba Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)
Shugaba Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)

Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da sace daliban a wata sanarwa da kakinsa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Lahadi.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumomin tsaron kasar da su kbutar da da ragowar daliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara.

A ranar Juma’ar da ta gabata wasu ‘yan bindiga suka fada wa wata unguwa da dalibai ke zaune a kusa da makarantar suka yi awon gaba da mutum 20.

Wasu rahotannin sun ce daliban sun kai 24.

Bayanai sun yi nuni da cewa mafi akasarinsu mata na yayin da rahotanni ke cewa an kubutar da shida daga cikin daliban.

Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da sace daliban a wata sanarwa da kakinsa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Lahadi.

“Babu wata hujja da ‘yan bindigar za su kafa kan sace daliban wadanda ba su ji ba ba su gani ba. Kawai laifinsu shi ne sun fita neman ilimi.

“Gwamnatin Tinubu na da nauyi da ya rataya a wuyanta na kare dukkan ‘yan Najeriya, kuma bisa wannan dalili, mu ke ba iyalan wadannan dalibai da aka sace tabbacin cewa, za mu dauki dukkan matakan da suka dace don ganin an kubutar da su lami lafiya.” Sanarwar ta ce.

Arewacin Najeriya, musamman wasu jihohin da ke yammaci na fama da matsalar ‘yan bindiga da ke kai hare-hare da sace mutane domin neman kudin fansa.

A baya, an sha sace daliban makaranta a sassan yankin inda akan kai ruwa rana kafina a kubutar da su.

A wasu lokuta, lamarin kan kai ga asarar rayuka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG