Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Titus Alams Ne Sabon Kakakin Majalisar Filato


Majalisar Dokokin Najeriya
Majalisar Dokokin Najeriya

Hakan ya biyo bayan janyewar tsohon kakakin majalisar John Clark Dabang.

Bayan an kwashe lokaci ana rikici a majalisar dokokin jihar Flato kan shugabnci, sakamkon rashin jituwa tsakanin wakilan majalisar da wani lokaci ake zargin da hanun bangaren zartaswa, majalisar dokokin jihar Flato ta rantsar da sabon kakakinta Mr.Titus Alams, mai wakilatar mazabar Bokkos.

Wannan mataki ya biyo bayan janyewar da tsohon kakakin majalisar John Clerk Dabang yayi. Ya gayawa wakilan cewa wannan shawara ta kashin kansa ne. Da kammala magana sai mataimakin kakakin majalisar John B. Shekarau, ya dare kujerar kakakin majalisar cewa shi zai jagoranci majalisa.

Nan da nan kuwa, dan majalisa Istifanus Monsat yace majalisa ba zata zauna ba domin bata da shugaba. Daga nan sai 'yar majalisa Zainab Dogo, ta gabatar da sunan Titus Alam a matsayin dan takara na shugabancin majalisa, ta sami goyon baya. Ba tareda bata lokaci ba, akawun majalisa ya rantsar da sabon kakakin majalisa.
Da yake magana sabon kakakin majalisar ya bayyana farin cikinsa ga dokacin wakilan majalsiar sabo da dama da suka bashi na jagoranci. Daga nan yayi kira ga wakilan majalisar su gudanar aikinsu kamar yadda ya kamata saboda muhimman ayyuka da suka hada da saka nazarin tsarin mulki, da batun taron tattauna ta kasa, da kuma rikicin Boko Haram.

Da gama jawabinsa sai wakili W. Abbas, mai wakiltar Dangi ya gabatar da kudurin a tsige mataimakin kakakin majalisar John Shekarau, wakilai 16 suka goyi bayansa. Aka gabatar da Madam Joyce mai wakiltar Langtang ta kudu a matsayin mai takarar mataimakin kakakin majalisa, ta kuma sami amincewar majalisa.
Ita ma aka rantsar da ita nan take.

Sabon kakakin majalisar Titus Alams, ya bayyana cewa majalisa zata yi zamanta na farko ranar 17 ga watan nan.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG