Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Da Biden Na Ci gaba Da Jan Hankalin Magoya Bayansu


Joe Biden da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump.

'Yan takarar shugabancin Amurka, Shugaba Donald Trump na jam'iyar Republican da tsohon Mataimakin shugaban kasa Joe Biden na Jam'iyar Democrat, na ci gaba da janto hankulan magoya bayan su ta lafuzaa da gudanar da ayyuka daban daban

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi yunkurin yin karin bayani jiya Alhamis kan jawabin da ya yi kwana daya da ya gabata da ya bukacin magoya bayansa su yi zabe sau biyu don su tabbatar an kirga kuri’ar su, jawabin da ya haifar da rudani game manufar sakon, da ya sa Facebook ya saka ikirarin nasa a matsayin mai kawo rudani.

A shafin Twitter jiya Alhamis, shugaban kasar ya ce su tura kuri’unsu ta hanyar aika wasiku sannan kuma su tafi runfunan zaben don duba cewa kuri’arku ta kai, kuma idan ba haka ba ka kada kuri’a da kanka, wannan zai tabbatar da kare ku’ri’u, yasha yin hasashe, ba tare da hujja ba cewa, za’a yi magudi a sakamakon, rashin kirga wasu kuri’u da kuma jinkirin da ba za’a lamunta ba.

Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “A ranar zabe, ko ka kada kuri’a da wuri, kaje runfunan zaben don ganin ko kuri’arku da kuka kada ta hanyar aikawa da wasika an kirga su. Idan an yi ba zaka iya yin zabe ba kuma tsarin aikawa da kuri’a ta wasika yana aiki yadda ya kamata. Idan ba’a kirga kuri’arka ba wanda wani hakki ne na ‘yan kasa,”

Da aka matsa mata lokacin da take ganawa da manema labarai jiya Alhamis kan ko ta amince karya doka ne a Amurka yin zabe sau biyu, sai sakatariyar yada labarai ta Fadar White House Kayleigh McEnany ta amsa akai-akai cewa, “Shugaban kasa bai yadda da jefa kuri’a ta hanyar da doka ta haramta ba.Sakatariyar yada labaran ta zargi kafafan yada labarai da sauya manufar jawaban Trump da wata manufa dabam.

A nasa bangaren, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Demokrat, Joe Biden, ya kai ziyara garin Kenosha da ke jihar Wisconsin jiya Alhamis, inda ya tattauna da al’ummomi a sakamakon tashin hankali jama’a da ya biyo bayan harbin wani bakar fata da wani farin dan sanda ya yi.

Kafin ya isa birnin mai mutane 100,000 da ke gabar tafkin Michigan, tsohon mataimakin shugaban kasar ya hadu da ‘yan uwan Jacob Blake a kusa da filin jirgin sama na Milwaukee. An harbi bakar fatar har sau bakwai a baya a ranar 23 ga watan Agusta yayin da ‘yan sanda suke kokarin kama shi kan sabanin cikin gida.

Ziyarar ta Biden na zuwa ne kwanaki biyu bayan da abokin karawarsa a zaben 3 ga watan Nuwamba, na jam’iyyar Refublikan shugaban kasa Donald Trump, ya ziyarci garin Kenosha tare da bayyana goyon baya ga jami’an tsaro da kuma kokarin su na kwantar da tarzoma da ta barke bayan da aka bar Blake da shanyewar barin jiki dan kadan yayin da suka yi artabu da ‘yan sanda. Trump bai hadu da dangin Blake ba yayin da ya ke Kenosha.

Kwamitin yakin neman zaben Biden sun ce shi da matarsa Jill Biden, sun gana da iyayen Blake da kuma wasu sauran danginsa, wasun su sun shiga ta wayar tarho, da aka shafe kusan sa’a daya ana tattaunawa. Sannan kuma lauyoyin Blake uku suma sun je wurin ko kuma sun kasance ta wayar tarho.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG