Shugaban na Amurka, ya ce yana duba yiwuwar mika bakin haure da ke tsare a kasar, zuwa biranen da suke ikrarin za su iya ba bakin hauren mafaka.
Wadannan birane sun kasance suna adawa da tsauraran matakan hana baki marasa takardun iznin zama shiga Amurkan.
A jiya Juma’a Trump ya fitar da wannan sanarwa, sa’o’i kadan bayan da Fadar White House da hukumar jami’an tsaron cikin gida ta Homeland Security, suka jaddada cewa an yi watsi da wannan shawara.
Amma yayin wata ganawar da ya yi da ‘yan jarida a jiyan, shugaba Trump, ya ce “yana matukar duba yiwuwar daukan matakin mika bakin hauren zuwa biranen da suka amince za su ba su mafaka.
Facebook Forum