Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Da Nancy Sun Caccaki Juna


Shugaban Amurka Donald Trump da kakakin Majalisar Wakilai Nancy Pelosi

Shugaban Amurka Donald Trump da kakakin Majalisar Wakilai Nancy Pelosi sun caccaki juna a jiya Lahadi, yayin da shari’ar da Majalisar Dattawa za ta yi a kan batun tsige shugaban ke karasowa.

Shugaban na Amurka ya kira Pelosi wacce ta yi ruwa da tsaki a kan batun tsige shi a Majalisar Wakilai mai rinjayen 'yan Democrat mahaukaciya Nancy, wato “Crazy Nancy”, kafin itama ta fadawa shirin This Sunday na ABC News cewa an tsige Trump har tsawon rayuwarsa koda kuwa shari’ar Majalisar Dattawan tazo karshe.

A watan da ya gabata ne, Majalisar Wakilai ta tabbatar da wasu kudurori biyu a kan tsige Trump, wadanda ke da nasaba da yunkurin tursasawa Ukraine ta gudanar da bincike domin amfanin kansa, lamarin da ke zama yin amfani da ofishinsa ta yadda bai dace ba da kuma hana Majalisar yin binciken huldarsa da Ukraine.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG